Ana ƙirga ƙuri’un zaɓen majalisar dokoki a Senegal

Spread the love

Ana ci gaba da ƙirga ƙuri’u a Senegal bayan zaɓen majalisar dokoki da aka yi wanda shugaban ƙasar ya kira a ƙoƙari da yake yi na samun goyon baya a majalisar domin aiwatar da sauye-sauyensa masu tsauri.

Bayan da ya ci zaɓen shugaban ƙasa a watan Maris, Bassirou Diomaye Faye, ya yi alƙawarin gudanar da sauye-sauye na tattalin arziƙi da tabbatar da adalci da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

Bayan da ya naɗa maigidansa na siyasa, Ousmane Sonko a matsayin firaminista, shugaban ya kasance cikin matsin lamba saboda rashin aikin yi na matasa da ke ƙaruwa.

Ana ganin babban kalubalensa a wannan zaɓe zai kasance ne daga tsohon shugaban ƙasar, Macky Sall, wanda a yanzu yake zaune a Moroko, kuma yana daga cikin haɗakar ‘yan hamayya.

 

Harin Isra’ila ya kashe aƙalla mutum arba’in da shida a Gaza – Jami’an lafiya

Jami’an kiwon lafiya a Gaza sun ce harin baya-bayan nan da Isra’ila ta kai ya yi sanadiyar mutuwar mutane aƙalla 46.

Mai magana da yawun hukumar tsaron farin kaya Mahmud Bassal ya ce mummunan harin ya faru ne a wani gini mai hawa biyar da ke yankin Beit Lahiya a arewacin Gaza.

Wakilin BBC ya ce wannan ya kasance ɗaya daga cikin hare-hare da ya kashe fararen hula mafi yawa cikin wata 13 uku da aka yi ana luguden wuta a zirin.

A wasu hare-hare daban-daban da Isra’ila ta kai, an bayar da rahoton an kashe Falasɗinawa goma a sansanin ƴan gudun hijira na Bureij da ke tsakiyar Gaza, da kuma wasu biyar a birnin Khan Younis a kudancin ƙasar.

Sama da mutum 30,000 aka yi wa magani a asibiti a Sudan

Jami’an kiwon lafiya a Sudan sun ce sama da mutum dubu talatin da uku suka sami kulawa a asibiti a birnin Khartoum tun bayan ɓarkewar yaƙin basasa a watan Afirilun bara.

Shugaban kwamitin gaggawa na kiwon lafiya ya ce an yi wa mutane sama da dubu ashirin aikin tiyata kyauta domin cire harsasai daga sassan jikinsu.

Yaƙin da ake gwabzawa tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun ƙungiyar RSF ya raba aƙalla mutane miliyan goma sha ɗaya da muhallansu a faɗin kasar Sudan.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu dari uku da arba’in ne suka tsere daga gidajensu a cikin watan da ya gabata kaɗai.

Shugaban gwamnatin Jamus ya kare tattaunawarsa da Putin

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya kare tattaunawar da ya yi ta waya da Shugaban Rasha, Vladimir Putin a shekaran jiya Juma’a abin da Ukraine ta bayyana rashin jin daɗinta a kai.

Yayin da yake bayani kan komawar Donald Trump fadar White House, Mista Scholz ya ce ba zai dace a ce Washington tana tuntuɓar Moscow akai-akai ba yayin da shugabannin ƙasashen Turai ke ƙaurace wa Rashar ba.

Mista Scholz ya ce a nasa ra’ayin, bai kamata a ce a yi zaman tattaunawa tsakanin shugaban Amurka da na Rasha ba a nan gaba, ba tare da shugaban wata muhimmiyar ƙasa ta Turai ya yi tasa tattaunawar ba.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button