An zabi Musiliu Akinsanya matsayin shugaban kungiyar direbobi ta NURTW
Tsohon shugaban kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa reshen jihar Legas, Mista Musiliu Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluomo, ya zama shugaban kungiyar na kasa.
Akinsanya ya zama shugaban ne bayan shi ne a zaben da ya gudana a sakatariyar kungiyar da ke titin Osogbo/Ikirun, a jihar Osun, ranar Asabar.
Wakilai daga jihohin Kudu maso Yamma da suka hada da Legas, Ogun, Ondo, da Ekiti ne suka halarci zaben.
Zaben wanda aka gudanar a yayin taron wakilan kungiyar na shekara hudu, mukaddashin shugaban kungiyar na kasa Aliyu Issa-Ore ne ya sanya ido a ya don tabbatar da anyi zaben lafiya.
Wakilan sun kuma zabi Tajudeen Agbede a matsayin mataimakin shugaban kungiyar na Kudu maso Yamma, da kuma Akeem Adeosun a matsayin mai rikon kwarya daga shiyyar.
Da yake jawabi bayan rantsar da shi, MC Oluomo ya bukaci ‘ya’yan kungiyar da su bashi hadin kai ya kuma kara jaddada aniyar sa na samun hadin kai a kungiyar.