An yi jinkirin fara buga wasan Bayern da Benfica na tsawon mintuna 15.
An jinkirta wasan na gasar cin kofin zakarun Turai tsakanin Bayern Munich da Benfica a ranar Laraba da mintuna 15 ne saboda cinkoson jama’a a hanyar zuwa filin wasan
An yanke shawarar baiwa magoya bayanta damar ne domin isa filin wasan kafin a fara bugawa
Bayern ta wallafa a shafinta na twitter cewa “saboda wahalar da magoya baya da yawa ke samu zuwa filin wasa, za a jinkirta fara wasan da mintuna 15”, yana mai kara da cewa “yanzu an warware matsalar”.
Jaridar PUNCH Online ta ruwaito cewa wasan ya tashi babu ci kuma ana cigaba da wasan a mintuna 45 kafin hada wannan rahoto.