An yankewa wani dan Najeriya hukuncin daurin shekaru 10 bisa zamba ta yanar gizo.

Spread the love

An yankewa wani dan Najeriya hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari na gwamnatin tarayyar Amurka bisa samunsa da hannu a wani gagarumin zamba ta yanar gizo da ya ci zarafin mutane sama da 400 a fadin Amurka wanda ya yi sanadin asarar kusan dala miliyan 20 baki daya.

Kafar Yada labarai ta VOA ta ruwaito cewa: Kamar yadda wasu takardu da shaidun kotu suka nuna, Babatunde Francis Ayeni mai shekaru 33 dan asalin Najeriya da ke zaune a kasar Burtaniya a lokacin da aka kama shi, ya shiga cikin wata gagarumar damfara ta hanyar amfani da imel da ya shafi hada-hadar gidaje a kasar Amurka.

A cikin watan Afrilun 2024. Ayeni ya amsa laifinsa na hada baki don yin zamba

A yayin zaman shari’ar na kwanaki da dama, Alkalin Kotun Amurka Terry Moorer ya ji tasirin wannan laifi daga kusan mutane ashirin da aka damfara.

Baya ga wadanda suka yi magana a gaban kotu, da dama daga cikin wadanda abin ya shafa sun ba da bayanin yadda laifin ya shafe su, tare da lura da cewa baya ga asarar duk kudaden da suka ajiye don sayen sabon gida, sun ji matukar kunya, yanke kauna, da kuma rashin jin dadi. da bacin rai saboda an cutar da su.

Wasu mutane da ke zaune a Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa ne suka hada baki domin aiwatar da wannan damfarar mai girma, inda ‘yan damfarar su ke aikawa kamfanonin saida gidaje da jami’ansu sakonnin email da wani wuri da za su matsa su shiga wani shafin boge na kamfanin saida gidaje, daga nan su samu su kutsa suna ganin wadanda su ke cinikin gidaje da su.

Yan damfarar suna aikawa da lambar ajiyar banki da suke bukata masu cinikin gidajen su tura kudin, sau da dama mutanen da kamfanonin basu ankara sai bayan sun tura kudin da babu hanyar da zasu samu a dawo masu da shi.

Fiye da mutane 400 a duk faɗin Amurka aka damfara ta wannan hanyar. Daga cikin wadannan, mutane 231 da abin ya shafa ba su iya soke tura kudin ta hanyar yanar gizo ba, ta haka su ka yi asarar kidin cinikin gaba daya.

Mutanen 231 da abin ya shafa suka yi asara asarar $19,599,969.46.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button