An samu raguwar kamuwa da cutar Malaria a duniya 2024

cutar Malaria a duniya 2024

Spread the love

Wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar ya nuna cewa an samu raguwar masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya a duniya, da kimanin mutum biliyan biyu inda aka samu raguwar masu mutuwa daga cutar tun daga shekarar 2000 kawo yanzu.

Sai dai rahoton ya ce har yanzu akwai miliyoyin mutane da ke fama da wannan cuta a duniya musamman a nahiyar Afirka, inda adadin masu kamuwa da cutar ya kai kashi 95 cikin dari, sakamakon rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya da kuma hanyoyin samar da kariya daga cutar.

Duk da wannan nasarar da aka samu a cikin wadannan Shekarau, Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayana cewa har yanzu cutar zazzabin cizon sauron na ci gaba da shafar mutane da dama a Afirka, musamman mata masu juna biyu da yara kanana wadanda su ne sahun gaba daga cikin masu fuskantar barazana daga wannan cuta.

Jaridar BBC News, Hausa ta ruwaito cewar Daga watan Nuwambar shekarar 2024, an samu kimanin kasashe arba’in da hudu da kuma wani yanki guda daya da suka zama na farko a duniya da hukumar lafiya ta duniya ta ce ta kawar da cutar maleriya dungurungum a cikinsu.

Kazalika, akwai kasashe da dama da ke daf da cimma wannan matsayi. Inda kimanin kasashen ashirn da biyar a yanzu daga cikin kasashe tamanin da uku da al’ummarsu suka fi fama da zazzabin cizon sauro, suka bayyana raguwar matsalar.

Daraktan hukumar Lafiyar, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce duk da an samu gagarumin ci gaba a wannan bangare na yaki da cutar maleriya a wasu sassan duniya, amma a kasashen Afirka har yanzu akwai fatan da ake da shi na neman mafita daga wannan barazana.

Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Adamawa ta dauki matakin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya 2024

Tun a shekarar 2015 WHO, ta ce an samu cimma kashi 16 cikin 100 na muradun da ake da sun a samun raguwar mace-mace a dalilin cutar ta Maleriya.

Sai dai wata kididdiga da hukumar ta fitar a 2023 ta nuna cewa a duk cikin mutum dubu daya ana samun kashi hamsin da biyu da ke mutuwa sakamakon cutar, abin da ke nuna karuwar masu rasa rayukansu fiye da sau biyu, wanda kuma ya yi hannun riga da muradin nan na shirin kawar da cutar maleriya nan da shekarar 2030.

A farkon wannan shekarar ministocin lafiya da ga kasashen Afirka sha daya da suka hada da Burkina Faso da Kamaru da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Ghana da Mali da Mozambique da Nijar da Najeriya da kuma Sudan, sun yi wani taro inda suka saka hannu kan wata yarjejeniyar da ke fafutukar yaki da maleriya da kuma manufar inganta tsarin kiwon lafiyar kasashen.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button