An gyara gidan mataimakin shugaban kasa Kashim kan kudi Naira Biliyon 5bn
Duk da tabarbarewar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki a fadin kasar nan, gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 5 domin gyaran gidan mataimakin shugaban kasa a jihar Legas.
A cikin kasafin kudi na N2.17tn da aka zartar a watan Nuwamba 2023, gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 3 domin gyara gidan mataimakin shugaban kasa a jihar Legas da kuma wani N2.5bn domin gyaran gidansa da ke cikin fadar Aso Rock Villa a Abuja. .
Sai dai binciken da wakilin Jaridar Punch ya yi ta hanyar amfani da GovSpend, wani dandalin da ke bin diddigin yadda gwamnatin tarayya ta ke kashe kudi, ya nuna cewa an kashe jimillar Naira miliyan 5,034,077,063 a watan Mayu da Satumba na wannan shekara domin gyara gidan maitaimaki shugaban kasa da ke Legas.
Takaddar kudaden da aka yi duk wata ya nuna cewa a ranar 31 ga Mayu, 2024, gidan gwamnatin jihar ya biya Naira miliyan 2,827,119,051 ga wani kamfanin, Denderi Investment Limited, domin gyara ofishin mataimakin shugaban kasa a Legas.
Hakazalika, a ranar 5 ga Satumba, 2024, ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya biya wannan kamfani N726,748,686 don ƙari akan aikin gyara gidan Kashim na Legas.
Ku tuna cewa a watan Nuwamba 2023, Hukumar Babban Birnin Tarayya ta ce za ta kashe N15bn don gina “madaidaicin” wurin zama na mataimakin shugaban kasa a Abuja.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai domin kare kasafin kudi na N61.5bn na birnin tarayya na shekarar 2023.
Sai dai wata kungiya mai fafutukar kare hakkin bil adama da lura kan tattalin arzikin kasa ta nuna rashin amincewa da kashe kudaden, inda ta bayyana hakan a matsayin wani kar ya kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma yaki da cin hanci da rashawa na kasa da kasa da kuma hakkokin bil’adama.
Babban daraktan cibiyar bayar da shawarwari ta CICLAC Auwal Rafsanjani, ya ce gwamnati mai ci ba gaskiya ta ke ba game da matakin da ta dauka na rage kudin gudanar da mulki, yana mai cewa da a ce da gaske za ta rage yawan kudaden da ake kashewa a kasafin kudinta daban-daban da ta aiwatar. a cikin watanni 16 da suka gabata.