An gano gawa 27 bayan kifewar kwale-kwale a jihar Kogi
Kwale-kwale: An gano gawa 27 a jihar Kogi
Hukumomi a Najeriya sun ce har yanzu ba a ga fiye da mutum 100 ba, bayan kifewar wani kwale-kwale ɗauke da sama da mutum 200 a jihar Kogi.
Har yanzu masu ninƙaya da ƙwararrun shiga ruwa na ci gaba da aikin ceto domin lalubo mutane da gawarwakin waɗanda suka mutu.
Cikin wata sanarwa da ofishin gwamnan jihar Kogi ya fitar, ya tabbatar da ceto aƙalla mutum 24, waɗanda yanzu haka ke karɓar magani a asibitoci.
Jaridar BBC Hausa Jami’an bayar da agajin gaggawa sun ce kawo yazu an lalubo gawarwaki 27 a daidai inda lamarin ya faru.
Kwale-kwalen – wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasuwar Katcha da ke ci mako-mako a jihar Neja – ɗauke da fasinjoji waɗanda galibi ‘yan kasuwa ne da manoma ya nutse a yankin Dambo-Ebuchi na Kogin Neja
Kawo yanzu ba a san musabbabin hatsarin ba. Akwai alamun da ke nuna cewa da dama daga cikin fasinjojin ba sa sanye da rigunan kariya lokacin faruwar hatsarin.
Hatsarin shi ne irinsa na uku da aka samu a Najeriya cikin wata biyu. A watan da ya gabata wani ƙaton kwale-kwale ɗauke da fasinjoji kusa 300 ya kife a tsakiyar Kogin Neja inda kusan mutum 200 suka rasa rayukansu.
Ko a makon da ya gabata wasu mutum biyar sun mutu bayan da wasu jiragen ruwa biyu suka yi hatsari a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.
Mutane akalla 200 ne ake fargabar sun mutu yayin da kwale-kwalen ya kife a Kogi
A ranar Juma’a ne wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji sama da 200 da ke kan hanyarsa daga al’ummar Dambo-Ebuchi a karamar hukumar Kogi ta jihar Kogi ya kife a kogin Neja, inda ba a tantance adadin fasinjojin ba.
Wadanda abin ya shafa, wadanda aka ce yawancinsu matan kasuwa ne, suna kan hanyarsu ta zuwa wata shahararriyar kasuwa a jihar Neja a lokacin da lamarin ya faru.
A cewar Daily trust Mazauna yankin sun ce kwale-kwalen ya samu matsala kuma ya nutse ne jim kadan bayan ya taso daga wani jirgin ruwa na yankin.
“Jirgin ruwan na wani Musa Dangana ne, kuma yana dauke da fasinjoji sama da 200, yawancinsu mata ‘yan kasuwa da ma’aikatan gona wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako ta Katcha a Jihar Neja daga Kogi,” wani dan yankin da ya bayyana sunansa da Abubakar, ya ce.
An gano cewa ya zuwa yanzu an gano gawarwaki takwas, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da kuma gano sauran fasinjojin.
Wata majiya mai tushe daga National Inland Waterways (NIWA) ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce, wadanda lamarin ya rutsa da su galibin matan kasuwa ne daga Kogi a kan hanyarsu ta zuwa wata kasuwa da ke jihar Neja.
Daily trust ta kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin kuma za a fitar da sanarwa a hukumance.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, SP Williams Aya, bai amsa kira ko sakon waya ba lokacin da aka tuntube shi.
Kwale-kwalen da ya yi wannan hadari wanda ke dauke ne da fasinjoji sama da mutum 200, ya rutsa ne da ‘yan kasuwa mata da masu aikin gona wadanda suka nufi kasuwar mako-mako ta Katcha.
Babu kuma wani daga cikin fasinjojin da hadarin ya rusta da su, da ke sanye da rigar kariya a lokacin hadarin ruwa, abun kuma da ke nuna fargaba kan yiwuwar samun yawan wadanda za su iya rasa rayukansu.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a tashar rarraba wutan lantarki da ake ginawa a jihar Kogi
Galibin mutanen dai sun fito ne daga Missa da ke a tsakiyar jihar Kogi mai makwabtaka da Neja, kamar yadda hukumomin agaji suka tabbatar.
Haduran jiragen ruwa dai ba sabon al’amari ba ne a Najeriya, inda a kullum ake dangantawa da gangancin daukar mutane da kaya fiye da kima.
Ko a cikin watan Oktoba ma dai an samu kwatankwacin hadarin nan a kwale-kwale a rafin Muwo Gbajibo da ke cikin karamar hukumar Mokwa na jihar ta Neja, inda mutane da dama suka rasu.