An fara taron majalisar dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP29

Spread the love

A ranar litinin ne aka buɗe taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP29 a Azerbaijan, wanda ke matsayin irinsa na farko da zai gudana bayan nasarar Donald Trump a zaɓen Amurka, cike da fargabar yiwuwar ya janye ƙasar shi daga ƙoƙarin da ake na yaƙi da ɗumamar yanayi.

 

Fiye da wakilcin ƙasashe 70 da ƙungiyoyi baya ga ƴan fafutukar yaƙi da matsalar ɗumamar yanayi ne yanzu haka suka hallara a birnin Baku fadar gwamnatin Azerbaijan don halartar taron na COP29 wanda ya faro a yau Litinin ake kuma fatan kammala shi ranar 22 ga watan nan.

 

Ana saran taron ya mayar da hankali kan barazanar da ke tunƙaro duniya bayan hasashen masana da ke gargaɗin cewa ana tunƙarar wani yanayi da ka iya zama mafi ƙololuwar zafin da duniya za ta fuskanta.

 

Tuni dai zaɓaɓɓen shugaban na Amurka Donald Trump ya sha alwashin fitar da ƙasar ta shi daga yarjejeniyar yanayi ta birnin Paris wadda ke da nufin rage tiriri mai guba da ke haddasa ɗumamar yanayi daga ƙasashe masu manyan masana’antu.

 

 

 

Mene ne COP29?

Ana kiran taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara kan sauyin yanayi, ”Conference of Parties”, ko COP kuma a takaice.

 

A wannan shekara za a gudanar da shi karo na ashirin da tara, wanda aka fara a birnin Berlin a shekarar 1995. Manufar taron na COP shi ne takaita fitar da iskar Carbon Dioxide (CO2) da kuma daƙile dumamar yanayi zuwa ma’aunin Celsius 1.5, matakin da a ke kafin bunƙasar masana’antu.

 

Wani muhimmin batu da za a tattauna a wannan shekara shi ne tara kuɗaɗe ga ƙasashe masu tasowa domin su iya tunkarar matsalar ɗumamar yanayi. Ƙasashe da dama sun riga sun fuskanci yanayi maras tabbas da gurɓacewar iska. Amma ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi na fuskanytar ƙalubale sauyi zuwa amfani da makamashi mai tsafta.

 

A shekara ta 2009, yayin da ake gudanar da COP15 a Copenhagen, an amince da cewa za a ware dala biliyan 100 a duk shekara daga ƙasashen da suka ci gaba don tallafaw ƙasashe masu tasowa su tunkari sauyin yanayi.

 

A shekarar 2015, an tabbatar da wannan adadin kuɗaɗen da za a yi aiki da shi daga 2020 zuwa 2025. A cewar rahotanni daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, an cimma burin tara dalar Amurka biliyan 100 a karon farko a shekarar 2022.

 

Bayan 2025, wani shiri na daban, mai taken “New Collective Quantitative Target on Climate Finance” (NCQG) zai fara aiki. Burin tara waɗannan kuɗa ɗe yana ɗaya daga cikin manyan batutuwa da za a tattauna a COP29 a Baku wannan watan.

 

Ƙasashe masu tasowa sun ce suna buƙatar kuɗaɗen da suka kai tsakanin dala tiriliyan 1.1 zuwa dala tiriliyan 1.3, amma ƙasashen da suka ci gaba suna son a bar wannan adadin a dala biliyan 100.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button