An dakatar da shugaban hukumar raya birnin tarayya Injiniya Shehu Hadi Ahmad.
Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), ya dakatar da Engr. Shehu Hadi Ahmad, Babban Sakataren Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA),
Babban mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa da sabbin kafafen yada labarai ga Ministan Lere Olayinka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
An kuma umarci Injiya Shehu ya mika mulki nan take bayan dakatarwar ta dindindin.
Ko da yake ba a bayar da dalilin daukar matakin ba, “Saboda haka an umurci sakataren zartarwa da aka dakatar da ya mika shi ga Daraktan na sashin Injiniya a ma’aikatar”
Falana ya soki Wike kan rabon gidaje ga alƙalai a Abuja
Femi Falana, lauyan kare hakkin dan’adam, ya soki Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya (FCT), kan baiwa alkalai gidaje.
A watan Satumba, ministan ya kaddamar da gina gidaje 40 don alkalai a Abuja, wanda ya tayar da hankula a cikin al’umma.
Ya ce daga cikin gidajen, 20 za a ware su ga alkalai na babbar kotun FCT, 10 kuma za a bai wa alkalai na babbar kotun tarayya, sannan 10 kuma ga alkalai na kotun daukaka kara.
TheCable ta rawaito cewa duk da haka, a ranar Laraba, Wike ya musanta zargin cewa gidajen ana ginawa ne don ya mallaki alkalai domin samun fa’ida ta siyasa.
Ya ce gina gidajen don alkalai wani bangare ne na shirye-shiryen walwala da Shugaba Bola Tinubu ya tsara don inganta ‘yancin bangaren shari’a.
A yayin da ya ke martani kan lamarin a wata hira da aka yi da shi a Politics Today, wani shirin talabijin na Channels, a ranar Laraba, Falana ya ce alkalai ba su da dalilin zuwa ga bangaren zartarwa don a saya musu motoci da gidaje.
Babban lauyan mai matsayin SAN ya ce cin gashin kai na bangaren shari’a ya kasance cikin kundin tsarin mulki.
Ya kara da cewa hukumar kula da fannin Shari’a ta ƙasa, NJC, ce ta kamata ta dauki nauyin raba gidaje ga alkalai ba ministan Abuja ba.