An ci tarar Bendel Insurance tare da kwashe musu maki
An ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Bendel Insurance tare da kwashe musu maki bisa karya dokokin tsaro da kuma cin zarafin alkalin wasa
Hukumar Kula da gasar Firemiya ta kasa , NPFL ta bayyana cewa Bendel Insurance za su yi asarar maki uku da kwallaye uku saboda cin zarafin jami’an wasa a yayin shan kashi da suka yi da 1-0 a hannun Kano Pillars a gida a ranar Asabar da ta gabata.
Hukumar gasar ta yanke wannan hukunci ne bayan ta karɓi rahoton wasan mako na 11 da aka buga a filin wasa na Samuel Ogbemudia, Benin City.
An kuma ci tarar kungiyar Naira miliyan biyu saboda kasa samar da tsaro mai kyau da inganci da kuma gazawar su wajen tabbatar da kyakkyawan hali daga masu goyon bayan su yayin wasan.
Kungiyar ta Benin City za ta biya wata tarar Naira miliyan daya saboda rashin da’a da ke iya kawo wa wasan zubar da kima.
Insurance na da sa’o’i 48 daga ranar sanarwa don ɗaukaka ƙara ga waɗannan takunkumin.
Ina nan a Saudi League, saboda a koyaushe ina son yin nasara, ba abu mai sauƙi ba ne wasa anan, amma ina fatan na lashe kofi nan ba da jimawa ba, wasu sun ce na zo Saudiyya domun samun kuɗi, ko kuma domin gasar mai sauƙi ce, Amma ni Ina nan ne domin ina sha’awar nan.” Ronaldo
Rafael Leao yana MAFARKIN komawa Barcelona – zai karɓi tayin da ƙungiyar za ta yi masa ba tare da wata shakka ba.
Kawo yanzu babu wata ƙungiya da ta haɗa yawan makin da Barcelona ta haɗa a manyan Lig-Lig guda biyar da sukai fice a nahiyar Turai.
Ruud van Nistelrooy ya bar Man United, bayan Amorim ya isa ƙungiyar
Ruud van Nistelrooy ya bar Man United, bayan Amorim ya isa ƙungiyar
Sabon kocin Manchester United Ruben Amorim ya isa Old Trafford yayin da ƙungiyar ta sanar da tafiyar kocin ruƙo Ruud van Nistelrooy, tare da mataimakan koci su uku.
Hukumomin Manchester United sun tabbatar da tafiyar Ruud van Nistelrooy kocin da ya yi wa ƙungiyar riƙon ƙwarya na ‘yan makonni, tare da mataimakansa guda uku, yayin da sabon koci Ruben Amorim ya iso yau Litinin.
Sanarwar da United ta wallafa a shafinta ta ce Nistelrooy zai cigaba da zama gwarzon ƙungiyar, kuma “Muna godiya da taimakonsa da kuma yadda ya yi aikinsa iya zamansa a kulob ɗin”.
Sauran jami’an horar da ‘yan wasa da suka bar United sun haɗa da Rene Hake, Jelle ten Rouwelaar da Pieter Morel. A yanzu United ta ce za ta sanar da jerin sabbin jami’an horar da ƙungiyar a nan gaba.
Yayin da sabon kocin Manchester United, Ruben Amorim yake isowa Old Trafford Litinin 11 ga Nuwamba, don fara aiki, masoya United za su kewar van Nistelrooy, wanda ya rike ƙungiyar tsawon wasanni huɗu bayan an sallami Erik ten Hag.
Tuni wasu masoya United da masu sharhi kan ƙwallo ke cewa ko ba komai Nistelrooy ya cancani zama a muƙami na biyu a ƙungiyar, ganin yadda ya jagoranci United wajen lashe wasanni uku da yin canjaras sau ɗaya.
A baya Nistelrooy mai shekaru 38, ya taɓa cewa zai zauna a United tare da sabon koci. Kuma nasarar da ya samu a ɗan lokacin da ya yi ruƙo ta saka fatan cewa yana hazaƙa da fahimtar ƙungiyar da ya taɓa bugawa wasa a baya.
Van Nistelrooy ɗan Netherland ne kuma gwarzo a tarihin tsaffin ‘yan wasan Man United. Shekaru kusan 20 bayan barinsa a matsayin ɗan wasa, ya dawo ƙungiyar da bazarar bana, a matsayin mai taimaka wa Ten Hag horar da ‘yan wasa.
Sai dai tuni sabon koci Amorim mai shekara 39 ya bayyana wa mahukuntan United cewa yana son mataimakansa a tsohon kulob ɗinsa na Sporting CP, Emanuel Ferro, Adelio Candido, da sauran jami’an horo su biyo shi zuwa United.
Sai ranar 24 ga Nuwamba ne sabon kocin zai jagoranci Manchester United a karon farko a wasansu da da Ipswich Town, wanda zai zo bayan hutun wasannin ƙasashen.