An bukaci ‘yan siyasa su kaurace wa sayen kuri’u – Abdussalami

Spread the love

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd), wanda shi ne Shugaban Kwamitin samar da zaman lafiya na kasa (NPC), ya bayyana hakan a lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba.

An gudanar da bikin ne a Akure, babban birnin jihar a ranar Juma’a. Aminiya ta ruwaito cewa ‘yan takarar jam’iyyun siyasa 17 da suka shiga zaben sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar.

Abdulsalami ya yi kira ga ‘yan takarar gwamna da su amince da sakamakon zaben matukar an yi shi cikin kwanciyar hankali, wadda ya ce hakan ne zai kawo zaman lafiya a jihar bayan an kammala zaben.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button