Amnesty ta zargi RSF da amfani da manyan maƙamai a yaƙin Sudan

Spread the love

Ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam ta Amnesty International ta zargi mayaƙan RSF da ke yaƙi da gwamnatin Sudan, da amfani da makaman Haɗaɗɗiyar Daular Laraba masu ɗauke da fasahar zamani ta sojin Faransa a yaƙin da suke ci gaba da gwabza wa da sojojin janar Abdel-Fattah al-Burhan a yankin Darfur.

Amnesty ta ce za a iya amfani da makaman domin keta hakkin ɗan’adam da ba su aikata laifin komai ba a yakin da ake yi a Sudan tun watan Afirilun bara.

Dakarun RSF karkashin jagorancin Janar Muhammad Hamdan Dagalo ko Hemeti sun karɓe iko da yawancin wurare masu muhimmanci a ƙasar Sudan.

Ambaliya na ci gaba da ɗaiɗaita birnin Malaga na Sifaniya

An tafka ruwan sama da ba a taɓa ganin irin sa ba cikin shekaru 35 a yankin Malaga na Sifaniya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da zagaye na biyu na ambaliyar ruwa cikin ƙasa da makonni uku.

Koguna sun cika sun batse, lamarin da ya tilastawa dubbai fice wa daga gidajensu.

A daren jiya an kwashe mutane 3000 daga gidajensu a yankin gaɓar teku, inda ambaliyar ta shafe titunan birnin Malaga.

Sai dai lamarin bai yi munin wanda aka gani a Valencia makonni biyu da suka wuce ba, inda sama da mutane 220 suka mutu.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button