Alhassan Yahaya ya zama sabon shugaban NUJ na kasa

NUJ

Spread the love

A ranar Larabar da ta gabata ne wakilan kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ suka zabi Alhassan Yahaya daga jihar Gombe a matsayin sabon shugaban kungiyar na kasa.

Yahaya ya samu kuri’u 436 inda ya doke abokan takararsa Dele Atunbi da Muhammed Garba wanda ya samu kuri’u 97 da 39 bi da bi.

A baya dai sabon shugaban NUJ ya taba zama shugaban kungiyar ta NUJ na jihar Gombe, mataimakin shugaban shiyyar Arewa maso Gabas, kuma har zuwa lokacin da aka zabe shi, ya kasance mataimakin shugaban kasa na kasa.

 

Labarai Masu Alaka

Najeriya na asarar sama da dala biliyan 1 kan cutar maleriya duk shekara – Minista

Zaben ya gudana ne a yayin taron wakilan kungiyar karo na 8 da aka gudanar a Owerri babban birnin jihar Imo a ranar Larabar da ta gabata.

 

Yahaya ya gaji shugaban kasa mai barin gado, Chris Isiguzo wanda yayi wa’adi biyu a shugaban jam’iyyar NUJ


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button