Akwai bukatar a zauna lafiya tsakanin manoma da makiyaya cewar -Sarkin Damaturu

Spread the love

Sarkin Damaturu, Dokta Shehu Hashimi II Ibn Umar Al-amin El-kanemi, ya yi kira da a zauna lafiya a tsakanin manoma da makiyaya a yankin tafkin Chadi, yana mai cewa hadin kai zai taimaka wajen samun ci gaban tattalin arziki da ake bukata.

Shehu ya yi wannan kiran ne jim kadan bayan taron ci gaban kasa da kasa na kwanaki uku da aka gudanar a birnin N’Djamena na jamhuriyar Chadi. Hakan na kunshe ne a cikin jawabinsa yayin taron masu ruwa da tsaki kan tattaunawa tsakanin manoma da makiyaya.

Sarkin ya bayyana cewa jihar Yobe ta samu zaman lafiya sakamakon kokarin da gwamnati ta yi tare da hadin gwiwar sarakuna nan gargajiya.

Ya yi kira ga manoman jihar da ma daukacin yankin Arewa maso Gabas da su fara aikin noma da wuri. Ya kuma ja kunnen makiyaya da manoma da kada su shiga tashe-tashen hankula.

A cewarsa, ya kamata a kiyaye zaman lafiya tsakanin kabilu daban-daban na yankin.

Dokta Shehu ya bukaci manoma da makiyaya da su zauna lafiya da juna kamar yadda ya umarci al’ummarsa da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya.

Shugabannin sun tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashensu da dadewa tare da lalubo hanyoyin inganta hadin gwiwa a bangarori daban-daban.

Sarkin ya shawarci manoma da makiyaya da su guji tashin hankali su rungumi tattaunawa wajen sasanta rikici, ya kara da cewa manoma da makiyaya na bukatar juna a kowane lokaci.

An ta tattaro cewa, sun kuma tattauna dabarun ci gaban addini, gargajiya da al’adu.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button