Kirsimeti: Kamfanin Aero ya rage kudin jirgi duk inda fasinja zai je
Kamfanin jiragen sama na Aero Contractors, wanda shi ne mafi dadewa a Najeriya, ya ce matafiya za su biya mafi ƙarancin N80,000 don tafiye-tafiyen cikin gida a wannan lokacin bukukuwan Kirsimeti.
Da yake magana da manema labarai a ranar Talata, Ado Sanusi, shugaban kamfanin jiragen saman, ya ce wannan farashin tikitin zai shafi duk hanyoyin da Aero ke zirga-zirga.
Sanusi ya bayyana cewa ta wannan mataki, wanda za a kammala a watan Janairun shekara mai zuwa, kamfanin na son ba da gudunmawa ga ‘yan Najeriya tare da tallafa musu a lokacin bikin Kirsimeti.
Da misalin ƙarfe 1:40 na rana a ranar Talata, tikitin aji na farko na Aero daga Legas zuwa Abuja yana kan N99,643, yayin da tikitin ajin kasuwanci ke kan N189,167.
Jirgi mara matuki na Isra’ila ya farmaki sojin wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya
Sanusi ya ce kamfanin ya yi nazari kan halin tattalin arzikin ƙasar, tare da tabbatar da cewa Aero zai ci gaba da samun riba duk da rage farashin.
Ya kuma ce jirage uku da kamfanin ke da su za su wadatar da duk ayyukansa, yana mai jaddada cewa Aero na da niyyar “ci gaba da kasancewa abin dogaro cikin sauƙi”. Daga jaridar Daily Nigerian Hausa