Adadin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu

Adadin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 33.88 a watan Oktoban 2024, daga kashi 32.7% a watan Satumbar 2024, wanda ke nuna karuwar kashi 1.18 a duk wata.

Spread the love

Adadin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 33.88 a watan Oktoban 2024, daga kashi 32.7% a watan Satumbar 2024, wanda ke nuna karuwar kashi 1.18 a duk wata.

Hakan na kunshe ne a cikin rahoton da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar a yau Juma’a.
Ofishin ya danganta hauhawar farashin kayayyaki da hauhawar farashin sufuri da kuma tsadar kayan abinci.

A kowace shekara, adadin hauhawar ya kasance maki 6.55% sama da adadin da aka samu a watan Oktoba na 2023 (27.33%).

Wannan na nuni da cewa hauhawar farashin kaya ya karu a watan Oktoban 2024 idan aka kwatanta da wannan watan a shekarar da ta gabata.

A kowane wata, hukumar ta kara da cewa, hauhawar farashin kaya a cikin watan Oktoban 2024 ya kai kashi 2.64%, wanda ya kai kashi 0.12% sama da adadin da aka samu a watan Satumban 2024 (2.52%).

Wannan yana nufin cewa a cikin Oktoban 2024, haɓakar farashi ya fi yawan karuwa akan matsakaicin farashi a cikin Satumba 2024.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button