Ma’aikatan kananan hukumomi a Abuja sun tsunduma yajin aiki kan rashin biyan mafi ƙarancin 70,000
Ma’aikatan kananan hukumomi a Abuja sun tsunduma yajin aiki
Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC reshen Abuja ta umurci dukkan ma’aikata a kananan hukumomi shida na babban birnin tarayya Abuja za su tsunduma yajin aiki na sai baba-ta-gani daga gobe 1 ga Disamba, 2024, kan rashin aiwatar da biyan mafi karancin albashi na N70,000 na kasa.
Shugaban kungiyar kwadago ta reshen Abuja, Kwamared Stephen Knabayi ne ya bayar da wannan umarni lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishin hukumar da ke Abuja, yau Asabar.
Ya ce kungiyar ta yanke shawarar umurtar mambobinta da su shiga yajin aikin ne sakamakon gazawar shugabannin kananan hukumomin shida na kasa aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000 na kasa, wanda a cewarsa ya sabawa doka kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.
Saboda haka dukkan ma’aikatan kananan hukumomi shida na babban birnin tarayya Abuja zasu shiga yakin aiki har sai an samu mafita.
Labarai masu alaƙa
Kungiyar ASUU ta bayyana shiga yajin aiki a jihar Bauchi
Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen jami’ar Sa’adu Zungur (SAZU) da ke Bauchi, zata shiga yajin aikin sai baba-ta-gani biyo bayan rashin biyan bukatunta da samar da kyakkyawan yanayin aiki daga hukumomin jami’ar.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan wani taron gaggawa da aka gudanar a harabar jami’ar Yuli da ke Bauchi, Shugaban kungiyar ASUU reshen jami’ar, Kwamared Awwal Hussain Nuhu, ya bayyana cewa majalisar ta garkame duk wata hanya da ta dace, da kuma kokarin ganin mahukunta su halarci taron. ga bukatunta ba su da amfani.
Shugaban majalisar ya ce majalisar ta lura da rashin shiri da jajircewar hukumar jami’ar da gwamnati wajen biyan bukatunta duk da kokarin da aka yi.
Nuhu ya ce, “Saboda haka, majalisar ta zartar da kudurin cewa reshen ya fara yajin aikin da ba za a iya yankewa ba har sai an sanar da shi.
“An umurci membobi da su fara yajin aikin gama-gari, kuma ba tare da wani dalili ba har sai an samu sanarwa. Wannan yana nuna cewa an dakatar da ayyuka kamar koyarwa, yin alama, tarurruka, ba da izini da duk wasu ayyukan da suka shafi ma’aikatan ilimi har abada.”
Dikko Radda ya amince da naira 70,000 mafi ƙanƙantar albashi a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ya amince da naira 70,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ga ma’aikata jihar.
Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce amincewar ta ƙunshi sake fasalin albashin ma’aikatan jihar ciki har da na ƙananan hukumomi da malaman makaranta.
Dikko Radda ya ce sabon albashin zai fara aiki daga watan Disamba mai kamawa.
”Ina miƙa godiya da jinjina ga ma’aikatan jihar Katsina bisa haƙuri da jajircewa da suka nuna, kuma ina kira a gare da ku ƙara jajircewa wajen aiki bisa gaskiya da riƙon amana…”, in ji gwamnan na Katsina.
A ranar Juma’a ne ƙungiyar NLC ta yi barazanar fara yajin aiki a wasu jihohin ƙasar ranar Litinin, ciki har da Katsina, saboda rashin amincewa da sabon tsarin albashin a jihohin.
One Comment