Abubuwan da Trump zai iya yi a ranarsa ta farko a White House
Donald Trump da Jam’iyyarsa ta Republican suna da manufa mai cike da buri kuma suna da kusan cikakken rinjaye a majalisar dokokin Amurka.
Trump ya ce zai ‘bayar da mamaki’ yayin da zai fara aiki cikin gaggawa bayan rantsar da shi a ranar 20 ga Janairu.
Tawagar sa ta ce a tsammaci kudurrori da dama da kuma umarni masu yawa – daga Ofishin shugaban Amurka – a cikin makon farko.
Masana siyasa da lauyoyi sun riga sun tsara waɗannan umarni a matsayin wani ɓangare na sauyin gwamnati.
Har yanzu,ƙungiyoyin fafutuka da gwamnonin jihohin da ke ƙarƙashin mulkin jam’iyyar Democrat sun sha alwashin ƙalubalantar aƙalla wasu daga cikin waɗannan tsare-tsaren.
Ga abin da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya ce game da abubuwan da ya sa a gaba a wa’adi na biyu.
Sakatariyar yaɗa labaran Trump Karoline Leavitt ta shaida wa Fox News a ranar Lahadin da ta gabata cewa mun san ya yi alƙawarin sanya hannu kan dokar kan dokar da za ta tabbatar da tsaro a iyakar kudancin ƙasar.
Mun san cewa a ranarsa ta farko zai ƙaddamar da korar baƙin haure mafi girma a tarihin Amurka, in ji ta.
A cikin mako guda da sake zabensa, Trump ya ba da fifiko wajen cike mukaman shugabancin ɓangarorin da zai sanya ido kan shige da fice, yana mai nuni da cewa yana shirin tunkarar shirinsa na manufofin kan iyaka cikin gaggawa.
Ya naɗa tsohon jami’in shige da fice Tom Homan a matsayin mai kula da harkokin kan iyaka; ya kuma zaɓi gwamnar Jihar South Dakota Kristi Noem don kula da tsaron cikin gida; sannan ya naɗa Steven Miller a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar White House kan manufofi.
Mista Miller ya shahara da tsara wasu shirye-shiryen Trump game da shige da fice ba bisa ka’ida ba a wa’adinsa na farko.
Duk wani shirin korar jama’a na iya fuskantar matsaloli a ɓangaren gudanarwa da kuma ɗimbin ƙalubalen shari’a daga masu ruwa da tsaki a harkar shige da fice da kuma masu fafutukar kare haƙƙin ɗan adam.
Trump na iya sake aiwatar da manufarsa ta Remain in Mexico wadda ta buƙaci masu neman mafaka su jira a Mexico yayin da ake aiwatar da ake sauraron buƙatunsu.
Shugaba Joe Biden ya kira shirin rashin mutunci kuma yayi ƙoƙarin kawo ƙarshensa a ranar farko da ya hau kan karagar mulki, amma ya fuskanci ƙalubalen shari’a. A 2022, Kotun ƙoli ta ba shi damar ci gaba.
A lokacin gwamnatin Trump, kimanin masu neman mafaka 70,000 ne aka mayar da su Mexico domin jiran sauraron buƙatun da suka miƙa.
Wani alƙawarin ranar farko da ya yi shi ne kawo ƙarshen zama ɗan kasa ta nayar haihuwa – dokar da ta shafe shekaru 150 da ta ce duk wanda aka haifa a ƙasar Amurka ɗan Amurka ne.
Ba a dai tabbatar da yadda Trump ke shirin cimma wannan manufa ba. Ya yi alƙawarin ba da umarnin amma kundin tsarin mulkin Amurka ya fayyace duk wasu shika-shikan zama ɗan ƙasa na
Zai buƙaci jihohi su amince da babban taron ƙasa ko kuma kashi biyu bisa uku na kuri’ar amincewa a majalisar dokoki don ba da shawarar kawo sauyi, sannan kuma a sami kashi uku bisa huɗu na majalisun dokokin jihohi wanda ƴan Republican ke da rinjaye a fiye da rabinsu.