Kasafin kudi: Nijeriya za ta ciyo bashin Naira tiriliyan 13 don cike gibin kasafin kudi na 2025 — Edun

Ministan Kudi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, ya bayyana a ranar Litinin cewa za a cike gibin naira tiriliyan 13 da ke cikin kasafin naira tiriliyan 48 na shekarar 2025 ta hanyar ciwo bashi.

Spread the love

Wale Edun, Ministan Kudi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, ya bayyana a ranar Litinin cewa za a cike gibin naira tiriliyan 13 da ke cikin kasafin naira tiriliyan 48 na shekarar 2025 ta hanyar ciwo bashi.

Nijeriya za ta ciyo bashin Naira tiriliyan 13 don cike gibin kasafin kudi na 2025 — Edun
Wale Edun

Ministan ya bayyana haka ne yayin da yake yi wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa bayani bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa jimillar kudaden shiga da aka tsara samu a shekarar 2025 za su kai naira tiriliyan 34.82, yayin da kudin kashewa aka yi hasashen zai kai naira tiriliyan 47.96, wanda ya karu da kashi 36.8 cikin dari idan aka kwatanta da kasafin 2024.

Gibin kasafin shekarar 2025 an kiyasta zai kai naira tiriliyan 13.14, wanda yake wakiltar kashi 3.89 cikin dari na GDP.

Edun ya ce an tsara kasafin ne bisa la’akari da irin cigaban da aka samu karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu a cikin watanni 18 da suka gabata.

“Kuma idan aka kalli lamarin daga matsayi na kasa da kasa, mu, kamar sauran gwamnatoci a duniya, muna damuwa kan yadda za mu cimma daidaiton kudi, tsakanin kudaden shiga da kashewa da kuma bashi da zai samar da yanayin da tattalin arziki zai iya bunkasa.”

Labarai masu alaƙa 

Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da kasafin kudi na 2025, wanda shugaba Tinubu zai gabatar.

Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da kasafin kudin Najeriya tiriliyan 47.9

Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da kasafin kuɗin Najeriya tiriliyan 47.9
Kasafin kudi

Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da kasafin kudi na 2025, wanda shugaba Tinubu zai gabatar.

Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da kasafin kuɗin Najeriya tiriliyan 47.9

Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala taron majaliar zartarwa a fadar shugaban Najeriya, a yau Litinin, ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu, ya ce kasafin kudi na 2025, an yi hasasshen za a kashe kusan naira tiriliyon 48. BBC Hausa.

Ministan ya ce an yi kasasfin kudi din ne kan farashin gangar mai dallar Amurka 75, tare da samar da gana sama da miliyan biyu duk rana, yayin aka yi hasashen farashin dalar Amurka kan naira 1,400. Kasafin kudi.

Minitan ya ce kuma an yi hasashen kuɗin shigar ƙasar kan kusan naira tiriliyon 35 na kasafin kudi.

Akwai alamun dake nuna cewa shugaba Tinubu ba zai gabatar da kasafin kudi a gaban Majalisar Dokokin ƙasar a gobe Talata ba kamar yadda aka tsara tunda farko. Kasafin kudi..

Ministan yaɗa labaran ƙasar Muhammed Idris ya ce shugabannin majalissun da ɓangaren zartarwa na aiki tare domin samar da ranar da za a gabatar da ƙudurin.

Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zantarwa ta tarayya yanzu haka a Abuja

Kasafin kudi: Nijeriya za ta ciyo bashin Naira tiriliyan 13 don cike gibin kasafin kudi na 2025 — Edun
ECOWAS

A halin yanzu dai shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ke jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Taron wanda ake sa ran zai kasance FEC na karshe a shekarar 2024, yana gabanin gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2025 da Shugaba Tinubu ya gabatar a ranar Talata.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Mista Femi Gbajabiamila; Shugabar Sabis na Tarayya, Misis Didi Walson-Jack; da kuma mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.

Haka kuma akwai mambobin majalisar ministoci da suka hada da Ministoci da ministocin kasa.

Taron FEC na karshe, wanda aka gudanar kimanin wata daya da ya gabata, ya amince da tsarin kashe kudi na matsakaicin wa’adi na Najeriya na shekarar 2025-2027 (MTEF), wanda ya hada da kasafin kudin shekarar 2025 na Naira Tiriliyan 47.9.

Shirin ya kunshi sabbin rancen Naira Tiriliyan 9.22 don samar da gibin da aka samu, inda farashin mai ya kai dala 75 ga kowacce ganga, inda ake hako ganga miliyan 2.06 a kullum, da kuma farashin canjin ₦1,400 zuwa dala.

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, wanda yanzu haka yake kasar Saudiyya don gudanar da karamin aikin hajji, bai halarci taron ba.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button