Za mu ceto arewa ne idan matasa suka karbi shugabanci – Bafarawa
Za mu ceto arewa ne idan matasa suka karbi shugabanci cewar Bafarawa
Tsohon gwamnan Sakkwato Alhaji Ɗalhatu Attahiru Bafarawa ya ce sun ƙaddamar da wata gwagwarmaya ta ceto arewacin Najeriya da kuma zaburar da matasan yankin.
A wannan makon ne, wasu jiga-jigan ƴansiyasa daga arewacin Najeriya suka ƙaddamar da wata tafiya da suka kira da sunan Northern Star Empowerment Initiative ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ɗalhatu Attahiru Bafarawa kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto.
Sun ce manufar ƙungiyarsu ita ce haɗa kan al’ummar yankin da ɗora matasa kan shugabanci.
A hirarsa da BBC, Alhaji Bafarawa ya ce sabon yunƙurinsu na da alaƙa da tsamo arewacin Najeriya daga matsalolin da yankin ke fama da su, kamar na taɓarɓarewar tsaro da rashin aikin yi da ƙaruwar fatara, baya ga ƙarancin abinci da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Akwai irin wannan ƙungiyar ta wasu manyan ƴansiyasar arewa da aka ƙaddamar ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, da ita ma ke iƙirarin samar da mafita ga arewa daga matsololin da yankin ke ciki musamman siyasa da tattalin arziki da zamantakewa.
Amma Attahiru Bafarawa ya yi iƙirarin cewa ƙungiyarsu ba ta siyasa ba ce.
“Ƙungiya ce mai zaman kanta, kuma ba ta siyasa ba ce, kuma ba ta da niyyar shiga siyasa, kungiya ce ta neman hakkin arewa,” in ji shi.
Ya rantse cewa yana jagorantar ƙungiyar ne ba da niyyar neman muƙami ba ko buƙatar tsayawa takara a zaɓe.
“Wallahi ba ni son a zaɓe ni, kuma ba ni son wani muƙami na gwamnati har bayan rai na, illa burina a ba samari haƙƙinsu domin a samu zaman lafiya,” a cewar Bafarawa.
Tsohon gwamnan na Sakkwato ya ƙara da cewa akwai hatsari idan har ana tauye haƙƙin matasa a Najeriya.
Ya ce akwai ɗimbin yara matasa a arewacin Najeriya amma an mayar da su baya saboda yadda wasu irin shi tsohon gwamna suka mayar da batun mulki kamar gado.
“Manufar wannan kungiyar shi ne yi wa matasa jagoranci domin ɗora su kan shugabanci, domin haƙƙisu ne muke ci.”
“Idan har muna son a zauna lafiya dole sai mun yi wa matasanmu jagoranci,” in ji shi
Ya ce duk wanda ya shiga kungiyar, kuma ya fito neman muƙami za su taimaka ma shi.
Ya ce kungiyarsu tuni ta samu goyon bayan malaman addini na musulmi da kirista da dama.
Ya ƙara da cewa an rarraba kan arewa ne ta hanyar surka ƙabilanci da addini domin raba musulmi da kiristocin yankin.
“Idan ba a yi amfani da addini ba, an san cewa arewa ba za ta taba watsewa ba har abada”
“Mun fahimci haka ne ya sa yanzu muka farga, domin mu tashi tsaye, kuma mu gyara wannan masifa da muka shiga,” in ji Bafarawa.
Ya jaddada cewa yankin arewa na fuskantar ƙalubale da dama wanda dole sai an fito da wasu sabbin hanyoyi da samar da haɗin kai tsakanin shugabanni da matasan yankin kafin samun ci gaba.
Yankin arewacin Najeriya dai na fuskantar tabarbarewar al’amura da koma-baya a fannoni da dama na ci gaba, musamman tsaro da ilimi da tattalin arziki.
Amma wasu masu sharhi sun bayyana wannan yunƙurin na ƙoƙarin farfaɗo da yankin a matsayin wata manufar siyasa, kuma ƙungiyar na iya rikiɗewa ta koma wata jam’iyyar siyasa idan tafiya ta yi tafiya, musamman la’akari da rarrabuwar kan shugabannin yankin.
Labarai masu alaƙa
One Comment