Maleriya: An samu raguwar kamuwa da cutar maleriya a duniya 2024

Wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar ya nuna cewa an samu raguwar masu kamuwa da cutar zazzabin maleriya na cizon sauro

Spread the love

Wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar ya nuna cewa an samu raguwar masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya a duniya, da kimanin mutum biliyan biyu inda aka samu raguwar masu mutuwa daga cutar tun daga shekarar 2000 kawo yanzu.

An samu raguwar kamuwa da cutar Maleriya a duniya
Sauro: Cutar Maleriya

Sai dai rahoton ya ce har yanzu akwai miliyoyin mutane da ke fama da wannan cuta a duniya musamman a nahiyar Afirka, inda adadin masu kamuwa da cutar ya kai kashi 95 cikin dari, sakamakon rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya da kuma hanyoyin samar da kariya daga cutar.

 

Duk da wannan nasarar da aka samu a cikin wadannan Shekarau, Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayana cewa har yanzu cutar zazzabin cizon sauron na ci gaba da shafar mutane da dama a Afirka, musamman mata masu juna biyu da yara kanana wadanda su ne sahun gaba daga cikin masu fuskantar barazana daga wannan cuta.

Jaridar BBC Hausa ta ruwaito cewar Daga watan Nuwambar shekarar 2024, an samu kimanin kasashe arba’in da hudu da kuma wani yanki guda daya da suka zama na farko a duniya da hukumar lafiya ta duniya ta ce ta kawar da cutar maleriya


dungurungum a cikinsu.

Kazalika, akwai kasashe da dama da ke daf da cimma wannan matsayi. Inda kimanin kasashen ashirn da biyar a yanzu daga cikin kasashe tamanin da uku da al’ummarsu suka fi fama da zazzabin cizon sauro, suka bayyana raguwar matsalar.

Daraktan hukumar Lafiyar, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce duk da an samu gagarumin ci gaba a wannan bangare na yaki da cutar maleriya a wasu sassan duniya, amma a kasashen Afirka har yanzu akwai fatan da ake da shi na neman mafita daga wannan barazana.

Tun a shekarar 2015 WHO, ta ce an samu cimma kashi 16 cikin 100 na muradun da ake da sun a samun raguwar mace-mace a dalilin cutar ta Maleriya.

Sai dai wata kididdiga da hukumar ta fitar a 2023 ta nuna cewa a duk cikin mutum dubu daya ana samun kashi hamsin da biyu da ke mutuwa sakamakon cutar, abin da ke nuna karuwar masu rasa rayukansu fiye da sau biyu, wanda kuma ya yi hannun riga da muradin nan na shirin kawar da cutar maleriya nan da shekarar 2030.

A farkon wannan shekarar ministocin lafiya da ga kasashen Afirka sha daya da suka hada da Burkina Faso da Kamaru da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Ghana da Mali da Mozambique da Nijar da Najeriya da kuma Sudan, sun yi wani taro inda suka saka hannu kan wata yarjejeniyar da ke fafutukar yaki da maleriya da kuma manufar inganta tsarin kiwon lafiyar kasashen.

Labarai masu alaƙa 

Ma’aikacin asibitin Kano ya dawo da N40m da ya tsinta

An yiwa akalla sojoji 656 murabus daga aiki

Hukumomin soji sun yi wa manyan hafsoshi 656 murabus

 

Sojojin da suka yi wa kasarsu hidima na tsawon shekaru 35, sun yi horon tsagaita wuta na tsawon watanni shida, kuma an sallame su daga aiki a cibiyar sake tsugunar da sojojin Najeriya (NAFRC) da ke Oshodi a Legas cikin hayaniya.

 

Sun hada da sojoji 535 na sojojin Najeriya (NA), 86 daga sojojin ruwa na Najeriya (NN), 35 daga rundunar sojojin saman Najeriya (NAF), da biyu daga hukumar leken asiri ta Najeriya (DIA).

 

Shugaban hafsan sojin sama (CAS), Air Marshal Hassan Abubakar, a lokacin da yake yabawa wadanda suka yi ritaya a bisa gagarumin hidimar da suke yi wa kasa, ya ce sakamakon jajircewar da suka yi, da jajircewarsu, da kuma tsayin daka a tsawon shekarun aikin da suka yi ya sa suka kammala karatun. .

 

Ya ce: “Ba shakka, wannan horon na watanni shida ya ba ku ilimi da basira don sauya sheka yadda ya kamata zuwa rayuwar jama’a, ku zama manajoji masu amfani, ’yan kasuwa, da masu bayar da gudummawa ga ci gaban kasa.

 

“Gaskiya taronmu na yau ya kawo tuna wa wani karin magana a cikin gida: ‘Soja ku zo, soja ku tafi, amma bariki ya rage’.

 

“Yayin da da yawa daga cikinmu na iya yin ba’a game da wannan magana yayin aikinmu, yana da ma’ana mai zurfi da ta cancanci tunani. Yana tunatar da mu cewa sojojin Nijeriya sun fi daidaikun mutanen da ke aiki a cikin su; cibiya ce mai tsayin daka da ke kare rayuwar al’ummarmu da kuma jure jarabawar zamani,” inji shi.

 

Ya ci gaba da cewa, a matsayin daya daga cikin ma’aikatan hidimar da suke rikidewa zuwa sabbin surori na rayuwa, dabi’u, al’adu, da tasirin hidimar da suke yi, suna ci gaba da tsara rundunar soji da kasa baki daya. Ya kara da cewa “Wannan karin maganar kuma tana nuna mahimmancin harsashin da kuka gina da kuma abubuwan da kuka bari a baya.”


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button