Hukumar Kwastam ta samu mace ta farko da ta zama matukiyar jirgi

Hukumar Kwastam ta samu mace ta farko mai tuka jirgi

Spread the love

Mataimakiyar Sufuritanda Kwastam (Mai tukin Jirgi) Olanike Balogun ta kafa tarihi a matsayin matar farko da ta zama matukiyar jirgi a Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS).

Hukumar Kwastam ta samu mace ta farko da ta zama matukiyar jirgi
Jami’a a hukumar kwastam

Ita dai Olanike ta taka rawar gani wajen karya shingaye a fannin zirga-zirgar jiragen sama.

An haifi Balogun a Kaduna, kuma asalin ta daga karamar hukumar Odo-Otin, Jihar Osun.

Tafiyarta ta fara ne a shekarar 2002 lokacin da aka dauke ta aikin Kwastam a matsayin Mataimakiyar Ma’aikaciya domin yin aiki a matsayin ma’aikaciyar cikin jirgi a sashen sufurin jiragen sama na hukumar.

Da take magana a wata hira kwanan nan, DSC Balogun ta bayyana yadda burinta mai karfi da tallafin Hukumar suka taimaka mata daga matsayin ma’aikaciyar jirgi zuwa samun lasisin zama matukin jirgi.

Ta ce, “Tsayawa a Hukumar lokacin da yawancin abokan aikina suka koma wuraren da ake biyan albashi mai tsoka a kamfanonin jiragen sama babban kalubale ne, amma na jajirce don ba da gudunmawata ga hidimar jama’a tare da cimma burina na zama matukin jirgi.”

Nasorinta a aiki sun hada da samun Diploma mai zurfi a fannin Tikitin Jiragen Sama da Ayyukan Ma’aikatan Cikin Jirgi, Digiri na biyu a Fannin Gudanar da Jama’a daga Jami’ar Ahmadu Bello, da kuma samun takardar shaidar zama matukin jirgi daga Flying Academy a Miami, Florida, da Hukumar Kwastam ta dauki nauyin horon.

Shugaban Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi, ya yaba da jajircewar ta, yana mai cewa nasararta shaida ce ta yadda Hukumar ke ba da muhimmanci ga inganta ma’aikata da sabbin hanyoyin ci gaba. Ya ce, “Labarin ta yana nuna abin da za a iya cimmawa da jajircewa da kuma tallafin hukuma.” daga jaridar Daily Nigerian Hausa.

Ƴan uwa 2 sun rasa ransu bayan sun ci rogo a Abuja

Wasu ‘yan’uwa biyu, Loveth Charles, ‘yar shekara 9, da dan’uwanta, Solomon Charles, mai shekaru 6, sun mutu bayan sun ci abinci da aka shirya da rogo.

An ce sun ci abincin tare da wasu ’yan uwansu.

Metro Abuja ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a unguwar Jiwa da ke babban birnin tarayya.

Daily trust ta ce Wani mazaunin yankin da ya so a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa, mahaifiyar ‘ya’yan biyu, Blessing Charles, da kuma danta, wadanda su ma suka ci abincin, suna kwance a babban asibitin Kubwa, inda aka ce an sallame su. ran juma’a.

Wata majiya daga cikin al’ummar ta ce wata manomiya ce ta kawo wannan rogon, wadda ‘yar asalin al’umma ce da mahaifiyar mamacin a jihar Delta.

Majiyar ta ce, “Matar mai suna Rita Francis, ta ajiye rogon ne a gidansu da ke kusa da gonarta, ba tare da sanin cewa ‘yan uwa sun kwashe rogon sun dafa ba.

Majiyar ta kuma bayyana cewa, matar da ta yi amfani da rogo wajen sarrafa “Apu” na sayarwa, tun daga lokacin da ‘yan sanda suka kama su tare da tsare su daga sashin Gwagwa, yayin da ‘yan sandan suka ajiye ragowar mutanen biyu a babban asibitin Kubwa.

Labarai masu alaƙa

Da aka tuntubi jami’in ‘yan sanda mai kula da sashin Gwagwa, CSP Muktar Adamu, ya tabbatar da faruwar lamarin.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button