Shekara 2 ina neman mutumin da ke damfarar mutane da suna na – Sheikh Abdallah

Damfara: Shekara 2 ina neman mutumin da ke damfarar mutane da suna na - Sheikh Abdallah

Spread the love

Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya baiyana cewa shi ma kusan shekaru biyu ya kwashe ya na neman Aminu Abdullahi, mutumin da ƴansanda su ka kama shi bisa zargin damfarar ƴan kasuwa a jihar Kano.

Shekara 2 ina neman mutumin da ke damfarar mutane da suna na - Sheikh Abdallah
An kama dan damfara

Rundunar ƴansandan jihar Kano a yau Laraba ta sanar da cafke Abdullahi, mai shekaru 50 da haihuwa bisa zargin amfani da sunan Sheikh Abdallah ya cuci al’umma.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama shi ne bisa korafe-korafen da wajen mutane 20 suka kawo cewa ya sayi kayan su amma bai tura musu kudin ta banki ba, inda ya ke ce musu zai aiko kuɗin an jima kuma shi ƙanin Sheikh Abdallah ne, don haka kar su damu.

Sai dai shi ma Sheikh Abdallah, a hirar da ya yi da Freedom Radio ya nuna takaicin yadda mutumin ke amfani da sunan sa ya na damfarar al’umma.

Shekara 2 ina neman mutumin da ke damfarar mutane da suna na - Sheikh Abdallah
An kama dan damfara

A cewar Sheikh Abdallah, mutane da dama sun zo wajen sa don bin bahasin kuɗaɗen su na kayan da su ka ce mutumin ya saya da sunan sa, inda malamin ya kara da cewa shi ba ya cim bashi kuma ba wani kaya da yanke siya bashi.

Shekara 2 ina neman mutumin da ke damfarar mutane da suna na - Sheikh Abdallah
An kama dan damfara

Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewar Sheikh Abdallah ya kuma yabawa rundunar ƴansanda bisa kamo mutumin, inda ya kuma yi kira ga al’umma, musamman ƴan kasuwa da su kiyaye kuma su dena yadda ana amfani da sunan sa wajen damfarar su.

Labarai masu alaƙa 

An yankewa wani dan Najeriya hukuncin daurin shekaru 10 bisa zamba ta yanar gizo.

Hukumar EFCC ta kama mutane 35 kan damfarar yanar gizo a Abia

 

EFCC: Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta sanar da kama wasu mutane 35 da ake zargi da damfarar yanar gizo a garin Aba na jihar Abia.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin hukumar EFCC akan X.com (tsohon Twitter) ranar Laraba.

A cewar hukumar EFCC, wadanda ake zargin sun hada da maza 34 da mace daya, a wani samame da suka kai da sanyin safiyar yau.

Jaridar Punch tace kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayoyin hannu guda 48, kwamfutar tafi-da-gidanka 9, wasu manyan motoci guda uku, agogon hannu, da fasfo na kasa da kasa.

Sanarwar ta ce, “Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta EFCC ta shiyyar Uyo a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, 2024, ta kama mutane talatin da biyar (35) da ake zargi da damfarar yanar gizo, wadanda suka hada da maza talatin da hudu da mace daya.

“An kama su ne a wani samame da suka kai da sanyin safiya a garin Aba, jihar Abia.

“Wadanda aka kama sune: Emmanuel James, Ukaomo Jefferson, Felix Onyema, Daniel Chimaobi, Chukwuemeka John, Prince Ogbonna, Charles Daniel, Emmanuel Igboanugo, Eric Uke, Emmanuel Ogechukwu, Chibuike Prosper, Obi Victor, Emmanuel Onwuchekwa, Price Kingsley, Uchechi Awo. , Chinonso Callistus, Edward Wisdom, Ejiogu Justice, Precious Edward, Moses Meshael, da Kalu Victor.

Ana zargin ɗan ƙasar China da karbar cin hanci na Naira miliyan 301.

Sauran sun hada da: Ujoatu Goodluck, Ikeh Sochima, Obinna Prosper, Onyekachi Christian, Christopher Chris, Precious Smart, Clinton Ifeanyi, Daniel Obuzoma, Chukwuebuka Promise, Cjay Ekeamaka, Ejiogu Price, David Favour, Okechukwu Emmanuel, da Nwigwe Joy.

“Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da: wayoyin hannu na zamani guda 48, kwamfutar tafi-da-gidanka tara, manyan motoci uku, agogon hannu, da fasfo na kasa da kasa.”

Kotu ta baiwa EFCC umarnin ajiye Yahaya Bello

Babbar kotun tarayya dake birnin Abuja ta mika ajiyar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a hannun hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (efcc).

Kotu ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga watan Disamba mai kamawa domin yin hukunci akan bukatar neman belin da tsohon gwamnan jihar Kogin, Yahaya Bello, da wasu mutum 2 suka gabatar mata.

EFCC ta shigar tuhumar zargin aikata almundahanar Naira biliyan 110 a kan tsohon gwamnan.

Bello yaki ya amsa tuhume-tuhume 16 da hukumar EFCC mai yaki da almundahana ke yi masa.

Tsohon gwamnan tare da Umar Oricha da Abdulsalam Hudu sun gurfana a gaban kotu a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa na 3, domin fuskantar tuhume-tuhume 16 da hukumar EFCC ke yi musu a kan badakalar naira biliyan 110.

Bayan da aka ji ta bakin wadanda ake karar, lauyansu, Joseph Daudu, ya gabatar da bukatar neman beli. Sai dai lauyan EFCC, Kemi Pinhero, ta kalubalanci bukatar, inda tace damar yin hakan ta kare tun a watan Oktoba.

Da yake karin haske, lauyan wadanda ake kara, yace bukata daya tilo dake gaban kotun ita ce ta neman belin wanda ake kara na 1, wacce aka shigar a ranar 22 ga watan Nuwambar da muke ciki.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button