Ɗan sanda ya yi sanadin mutuwar ƙanwar gwamnan Taraba 2024
Antsinci, ƙanwar Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ta rasu bayan samun raunin harbin bindiga da wani ɗan sanda ya yi mata.
Antsinci, ƙanwar Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ta rasu bayan samun raunin harbin bindiga da wani ɗan sanda ya yi mata.
Ko da yake ba a sanar da rasuwarta a hukumance ba, rahotanni sun ce ta rasu a wani asibiti da ba a bayyana sunansa a Abuja, inda ake duba lafiyarta bayan faruwar lamarin, kamar yadda Trust radio ta rawaito. Dan sanda
Lamarin, ya faru ne a ranar 5 ga watan Disamba, lokacin da wasu mahara a kan babura suka kai wa tawagar motocin mahaifiyar gwamnan, Jummai Kefas, hari a kan hanyar Wukari-Kente a jihar. Dan sanda.
Lokacin harin, wani ɗan sanda mai gadin tawagar ya yi ƙoƙarin harbin mahara da suka so tare hanyar motar da ke ɗauke da mahaifiyar gwamnan, amma harsashin ya samu Atsi, wadda ta ke zaune kusa da mahaifiyarta. Dan sands.
An garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Wukari, amma daga baya aka tafi da ita Abuja domin ba ta kulawa ta musamman. Dan sanda.
Wata majiya a gwamnatin jihar, ta tabbatar da rasuwarta, amma ta ce ba a sanar da labarin rasuwar a hukumance ba.
Kowane ɗan Najeriya na da damar takarar shugaban ƙasa a kowane lokaci – Atiku
Wasu kalamai da suka fito daga bakin sakataren gwamnatin Najeriya, George Akume, na neman ‘yan siyasar arewacin ƙasar su jira har shekarar 2031 idan suna son yin takarar shugabancin ƙasar, sun janyo cece-kuce.
Mista Akume, ya faɗi hakan ne yayin hira da wani gidan talabijin a ƙasar, inda ya ce kamata ya yi a bar yankin kudancin Najeriya ya karasa shekaru takwas ɗin sa, kamar yadda itama Arewa ta yi lokacin mulkin shugaba Buhari.
Kalaman dai sun girgiza ƴan siyasar arewacin Najeriya, inda tuni aka fara mayar da martani.
Mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Abdulrashid Shehu Uba, ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowaye damar fita don neman kujerar shugaban ƙasa.
“Babu wata yarjejeniya da aka yi ko kuma aka yadda za a tafi a kan wannan tsari. Idan su a APC sun yi wannan tsari mu ba haka yake a wajenmu ba. Ya kamata su tsaya su mayar da hankali kan zaɓen da suka ƙwace,” in ji Abdulrashid.
Kakakin na Atiku ya ce kowa na ganin yadda al’amura suka taɓarɓare a yanzu musammman ɓangaren tsaro da kuma tsadar rayuwa, inda ya ce da gwamantin APC ta yi aiki ba za ta fito ta ce kada wani ya yi takara ba.
Ya ce babu wani ɗan siyasa da suke tsoro kamar tsohon mataimakin shugaban ƙasar.