Ɓarayi sun sace injinan jan ruwa na kimanin Naira miliyan 1 da sauran kayayyaki a makarantar firamare a Kano

ɓatagari

Spread the love

Wasu ɓatagari  da ba a san ko su waye ba na ta aikata sace-sace a makarantar firamare ta Yalwa Model, da ke karamar hukumar Dala a jihar Kano, inda su ka sace kayayyaki masu muhimmanci da masu tsada na miliyoyin naira.

Da ya ke bayani ga manema labarai a Kano a yau Litinin, shugaban makarantar, Malam Umar Aliyu, ya ce wannan al’amari ya faru ne a cikin kankanin lokaci tun lokacin da aka tura shi makarantar a matsayin shugaban makaranta kwanan nan.

A cewarsa, batagarin sun yi amfani da gajeruwar katangar da ke kewaye da makarantar don

makarantar firamare
makarantar firamare

 

Ya baiyana cewa ɓarayin sun yi awon-gaba da injinan jan ruwa guda biyu da farashin ko wanne ya kai Naira dubu 500, inda aya kara da cewa wasu ƙungiyoyin taimakon al’umma ne su ka kawo makarantar

Labarai Masu Alaka

ANZU-YANZU: Tinubu ya soke aikin gyaran hanyar Abuja, Kaduna, Zaria zuwa Kano

 

“Hakazalika sun haura ofishi na kuma da su ka ga babu abin da za su iya sata, sai suka cire duk wayoyin da ke ofishina suka shiga ɗakin kwamfutoci ta rufin. A nan ne suka saci kaya masu amfani.

“Sun kuma yi ƙoƙarin sace janaretan mu babba, amma saboda nauyinsa, muna tsammanin hakan ne ya sa ba su iya ɗauka ba, sai suka cire wayoyin kwayil din sa su ka ta gudu.”

makarantar firamare
makarantar firamare

Ali ya kuma koka kan rashin tsaron da ya dace a makarantar, inda ya bayyana cewa masu tsaron da ke akwai tsofaffi ne.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta ɗauki matakan gaggawa ta samar da matasa masu ƙarfin jiki don tsaron makarantar.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button