Ƴansanda sun kama mutum 82 da ake zargi da aikata laifuka a Kano
Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Kano ta kama mutum 82 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin jihar daga ranar 1 ga Nuwamba zuwa 14 ga Nuwamba.
Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Kano ta kama mutum 82 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin jihar daga ranar 1 ga Nuwamba zuwa 14 ga Nuwamba.
Wadanda aka kama sun hada da masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami, ‘yan daba, masu satar wayoyi, da masu safarar miyagun kwayoyi.
Da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar rundunar da ke Bompai, Kano, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce an samu nasarar cafke wadannan mutane ne sakamakon dabarun yaki da laifuka da rundunar ta aiwatar.
“Aiwatar da wadannan dabaru ya haifar da sakamako mai kyau, inda aka samu nasarar ragargaza cibiyoyin laifuka kamar dakile ragowar ayyukan ‘yan daba a cikin birnin Kano.
“Sauran nasarorin sun hada da tarwatsa kungiyoyin ‘yan fashi da makami a kan iyakokin Jigawa-Kano da Bauchi-Kano, da kuma hana aukuwar garkuwa da mutane a kan iyakokin Kaduna-Kano da Katsina-Kano.”
One Comment