Rundunar ƴansanda a Kano ta kama mutum 3 da jabun kudaden ƙasar waje
Rundunar Ƴansanda ta Jihar Kano ta yi holon wasu mutane uku da ake zargi da samun su da jabun kuɗaɗen ƙasar waje na kimanin Naira biliyan 129.
Da ya ke jawabi ga manema labarai, Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce kuɗaɗen sun haɗa da Dalar Amurka miliyan 3, 366, 000, sai kuma sefa miliyan 51, 970,000 sai kuma kudin Nijeriya Naira miliyan 1, 443.
Kiyawa ya ce ko a baya ma sun taba kama irin waɗannan masu lefin, inda ya kara da cewa rundunar ba za ta amince da irin wannan ta’ada ba.
Ya kuma baiyana gagarumin ci gaba wajen rage yawaitar aikata laifuka a fadin jihar, ta hanyar amfani da dabarun hadin gwiwa wanda ya hada da tsaron al’umma, ayyukan bincike na sirri, da kai farmaki kan maboyar masu aikata laifi.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewar A cewar Kwamishinan ‘Yansanda, CP Salman-Dogo Garba, rundunar ta samu nasarar kama mutane 62 da ake zargi da aikata manyan laifuka, ciki har da fashi da makami, garkuwa da mutane, da kuma satar shanu, daga ranar 25 ga Nuwamba zuwa 9 ga Disamba, 2024.
CP Salman-Dogo Garba, wanda ya yi jawabi ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a hedkwatar ‘yansanda da ke Bompai, Kano.
Ya bayyana cewa manyan nasarorin da aka samu sun hada da kama mutane takwas da ake zargi da fashi da makami, mutane goma da ake zargi da satar shanu, da kuma mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da mutane.
An ceto mutum guda da aka yi garkuwa da shi da kuma wani mutum daya da aka sace, baya ga mutane 10 da aka ce suna karkashin cinikin mutane.
Kiyawa ya kuma bayyana cewa, idan akwai gaggawa ko bukatar kai rahoton wani abin da ake zargi, ana iya tuntuɓar rundunar ‘yan sanda ta Kano ta wadannan lambobi: 08032419754, 08123821575, da 09029292926.
Kwamishinan ‘yan sanda ya godewa Gwamnatin Jihar Kano, sauran hukumomin tsaro, da masu ruwa da tsaki a al’umma bisa goyon baya da hadin kan da suke bai wa rundunar.
Labarai masu alaƙa
Yan sanda a Kano sun kuɓutar da ƴar shekara huɗu daga hannun masu garkuwa 2024
Ministoci 2 sun halarci taron bai wa matasa 1000 tallafi a Kano
Ministar Harkokin Mata, Imaan Sulaiman, da Ministan Ci gaban Matasa, Ayodele Olawande, sun halarci taron ne, domin shaida bai wa matasa 1000 tallafi na Naira 50,000, a cewar jaridar trust radio.
Mamba a Kwamitin Gudanarwa na Kwalejin Ilimi (FCT), Potiskum, Yobe, Nasir Bala Ja’oji, ya shirya bayar da tallafi ga matasan.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Ja’oji ke bai wa matasa da mata tallafi ba.
A watan Satumban 2024, ya tallafi kimanin mutum 484 tallafi na kuɗi.
A rabon tallafi ga matasan, mutum huɗu, sun amfana da Naira miliyan ɗaya kowannensu, yayin da mutum 200 suka samu Naira 100,000 kowanne.
Har ila yau, mutum 100 sun samu Naira 50,000 kowanne, wasu kuma 100 sun samu Naira 20,000 kowanne daga tallafi na kudin.
Haka kuma yabayar da tallafi ga mutum 30 sun samu babura, yayin da 50 suka samu keken ɗinki.
Da ta ke jawabi a wajen taron, Ministar Harkokin Mata, Imaan Sulaiman, ta bayyana cewa wannan tsari ya nuna karfin haɗin kai da jajircewa wajen bayar da tallafi wa mata da ci gabansu.
“Yayin da muke murnar bayar da tallafi wa matasa da mata 1,000 a yau, muna tunatar da kanmu cewa har yanzu akwai aiki da yawa a gaba.
“Duk da haka, tare da jagoranci da hangen nesan Shugaba Tinubu, muna da ƙwarin gwiwar cewa Najeriya za ta ci gaba da samun nasarori wajen ganin ya tallafi mata.
“Ina yaba wa Honarabul Ja’oji saboda ƙoƙarinsa wajen tallafi wa matasa da mata. Shirinsa na wannan tallafi yana nuna kishinsa wajen bai wa mata damar cin gajiyat tattalin arziƙin ƙasa.”
Ta ƙara da cewa ma’aikatarta a shirye ta ke don yin aiki tare da Ja’oji da sauran masu ruwa da tsaki don ci gaban mata.
A nasa ɓangaren, Ministan Ci gaban Matasa, Ayodele Olawande, ya yaba wa Ja’oji saboda tallafa wa matasa.
Ya ce irin wannan shiri ya dace da manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu na tallafa wa matasa.
“Mun yi imanin cewa tare da haɗin gwiwa, za mu iya gina kyakkyawar makoma ga matasan Najeriya. Ma’aikatarmu tana jajircewa wajen tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta ci gaban matasa, kasuwanci, da ƙirƙire-ƙirƙire.
“Irin wannan ƙoƙari abin koyi ne ga duk wanda ke sha’awar samar da ci gaba. Muna fatan cewa dukkanninmu za mu haɗa kai don ganin cewa matasa suna samun dama mai kyau don cimma burinsu.”
Tun da farko, Nasir Bala Ja’oji, ya bayyana cewa wannan taro wani ɓangare ne, na burinsa na tallafa wa matasa da mata don ci gaba da goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ina farin cikin sanar da ku cewa, a baya-bayan nan na bayar da tallafin Naira miliyan 88 ga gamayyar matasan APC na Kano don ƙara wa wannan ƙoƙari armashi. Burina shi ne ci gaba da bai wa shugaban ƙasa gudunmawa don cimma manufofinsa.
“Mun tsara wannan shiri ne domin rage raɗaɗin matsalolin tattalin arziƙi da ake fuskanta. Ta hanyar tallafa wa matasa da mata, ba wai kawai muna inganta rayuwarsu ba ne, har ma muna bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa.”
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, Daraktan Cibiyar Samun Nasara ta Ƙasa, Baffa Babba Danagundi, da sauransu.