Ƴan siyasa ne su ka talauta yankin Arewa sama da shekaru 40 – Dogara
Dogara: Yan siyasan arewa su suka talauta yankin a cewar Yakubu Dogara
Tsohon kakakin majalisar wakilai ta 9, Yakubu Dogara, ya danganta abinda aka samu na koma bayan da Arewa ke fuskanta a halin yanzu ga shugabanninta.
Dogara ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su marawa shugaba Bola Tinubu baya wajen kawo sauyi ga al’ummar kasar ta hanyar kudirin gyaran haraji da ke jiran amincewar majalisar dokokin kasar a halin yanzu.
Dogara ya yi wannan maganar ne a wani taro da aka yi na shugabannin Kiristoci a arewacin Najeriya.
Taron mai taken “Choci da Al’umma: Gyaran Haraji da Matsalolin da ke cikinta”, an kuma tattauna batutuwan da suka shafi shugabanci da ci gaba.
Tsohon shugaban majalisar ya koka kan yadda shugabannin siyasar Arewa suka yi amfani da damar da suka samu na shugabancin Najeriya sama da shekaru 40, lamarin da ya ke tunanin ya jefa yankin cikin talauci da rashin ci gaba.
A cewar Dogara, kamata yayi ’yan Arewa su yi watsi da yunƙurin ɗora wa Shugaba Tinubu alhaki game da halin da Arewa ke ciki a halin yanzu. Daily Trust
Ya kuma jaddada bukatar a hada karfi da karfe wajen tallafawa kudirin gyaran haraji, wanda ya ce an tsara hakan ne domin kawo sauyi ga Arewa da Najeriya baki daya.
A yayin taron wani yayi tambaya inda ya bashi amsa Wasu suna ikirarin cewa Yarabawa suna samun mukamai, amma a tuna cewar yan Arewa sunyi mulkin kasar nan sama da shekara 40.
Da yake magana kan kudaden harajin da kason kudin tarayya da jihohi ke karba, Dogara ya soki gomnonin Arewa inda yace sun yi almubazzaranci da su a maimakon saka hannun jari wajen samar da ci gaba mai ma’ana.
Ya kuma bayar da misali na inganta masana’antar karafa ta Ajaokuta da gwamnatin Shagari ta kaddamar, wanda kashi 98 cikin 100 an kammala shi amma daga baya aka bar shi ya tabarbare.
Dogara ya bukaci ’yan Arewa da su marawa yunkurin Shugaba Tinubu baya na kawo sauyi a kasar ta hanyar bayar da goyon baya na kudurorin gyara haraji a Majalisar Dokoki ta kasa.
Da yake jawabi Babban Daraktan Cibiyar wayar da kan jama’a ta Nijeriya (CHAIN), Reverend Joseph John Hayab, ya bukaci shugabannin kiristoci da su samar da mafita kan batun sake fasalin haraji da bangaren majalisar dokokin Najeriya ke nazari akai a halin yanzu.
Labarai masu alaƙa
Wutar lantarki ta sake lalacewa a Nijeriya
One Comment