Ƴan APC sama da miliyan 26 sun yi barazanar ficewa daga jam’iyyar
Ƴan APC 26 sun yi barazanar ficewa daga jam'iyyar
Kungiyar ‘Team New Nigeria’ (TNN) ta fara shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar APC don kafa sabuwar jam’iyyar siyasa da za ta ceto Najeriya daga talauci, yunwa, rashin tsaro da lalacewa.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa ƙungiyar ta bayyana cewa tana da mambobi masu rijista har miliyan 26,382,000 daga sassan ƙasar nan, waɗanda su ka amince su gina sabuwar Najeriya ba tare da rashin shugabanci mai kyau, son kai, da jami’an gwamnati masu cin hanci da rashawa ba.
Shugaban kungiyar, Modibbo Yakubun Farakwai, ne ya bayyana haka yayin kaddamar da kwamitin haɗin kan ƙungiyar na jihar Kano a hukumance a Kano a yau Litinin.
Me ya sa APC ke son a hana ƙananan hukumomin Kano kuɗin wata-wata?
“Mun fahimci cewa mutanenmu suna matuƙar buƙatar sauyi, amma ba kawai sauyin gwamnati suke nema ba. Suna neman jam’iyyar siyasa da za ta kawo sababbin fuska domin maye gurbin tsofaffin shugabanni. ‘Yan Najeriya suna son ganin sauyi a al’adar gudanar da mulki da ingancinsa. Suna son ganin gaske a tsarin yadda gwamnati ke aiki a duk matakai.
“Ina so in yi amfani da wannan dama in gaya muku cewa da goyon bayan ku, TNN za ta samar ba kawai wata gwamnati madadin ba, har ma da wata al’adar mulki madadin, wacce aka tushen ta a kan ƙa’idar dimokuradiyya,” in ji shi.
APC za ta daɗe tana mulki a Najeriya – Ganduje
Shugaban APC Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi hasashen cewa yadda jam’iyyar ke ƙara farin jini da samun karɓuwa a Najeriya alama ce da ke nuna cewa za ta daɗe tana mulki a ƙasar.
Hasashen na Ganduje na cikin wata sanarwa ne da babban sakataren yaɗa labaransa Edwin Olofu, ya fitar a yau Lahadi a Abuja, a kan sake zaɓen Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo da aka yi.
Shugaban jam’iyyar ta APC na ƙasa ya ce sakamakon zaɓukan jihar Edo da kuma yanzu na Ondo, alama ce ta cewa ‘yan Najeriya sun rungumi jam’iyyar mai mulki a ƙasar.
A yau Lahadi ne hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta bayyana Gwamna, Lucky Aiyedatiwa na APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen da aka yi jiya Asabar, da ƙuri’a 366,781, inda zai ci gaba da wa’adinsa na biyu, bayan ya kada babban abokin hamayyarsa Agboola Ajayi na PDP wanda ya samu ƙuria’a 117,845.
Jam’iyyar PDP ta soki sakamakon zaɓen na Ondo da cewa shi ne mafi muni da INEC ta taɓa yi – babban sakataren watsa labaranta Debo Ologunagba ya ce an yi amfani da kuɗi wajen sayen kuri’a fiye da hankali, baya ga tarin maguɗi.
Yahudawa masu bin addinin gargajiya na zanga-zanga kan sa su aikin soji a Isra’ila
Yahudawa masu bin addininsu na gargajiya da ke zanga-zangar ƙin yarda da shirin gwamnatin Isra’ila na tilasta shigar da su aikin soja sun datse babban titin da ke kusa da birnin Tel Aviv.
Matakin nasu ya biyo bayan umarnin da aka bayar a yau Lahadi na tura sababbin rukunin waɗanda za a sa aikin na soji maza daga cikin al’ummar Yahudawan na Haredi.
A ka’ida ba a shigar da su aikin soji idan suna cikin karatun addini ka-in-da-na-in. To amma a wata Yuni yayin da rikicin Gza ya tsananta sai kotun ƙolin Isra’ila ta kawar da wanan doka.
Yahudawan masu bin addinin gargajiya sun kafe cewa aikin soja na barazana ga harkokinsu na addini da wanzuwar al’ummarsu.