Ƙungiyar ƴan ƙabilar Igbo ta Ohanaeze ta buƙaci gwamnatin tarayya ta kawo ƙarshen Lakurawa

Spread the love

Kungiyar koli ta al’adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta koka kan bullowar sabuwar kungiyar ta’addanci da ke dauke da makamai ta Lakurawa a jihohin Kebbi da Sokoto da ke Arewa maso Yamma, inda ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa kafin ta karu.

A wata sanarwa da babban sakataren kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro ya fitar a ranar Talata, kungiyar ta Igbo ta bayyana cewa, sabuwar kungiyar na da wata barazana, ba wai kawai ga tsarin mulkin kananan hukumomi ba, har ma da rayuwar ‘yan kabilar Igbo da ke zaune a yankin

A yanzu wadannan ’yan ta’adda suna zama masu shari’a da kansu, suna tsoma baki a harkokin shari’a da gudanar da shari’o’in da ba bisa ka’ida ba a karkashin inuwar shugabannin gargajiya.

Dangane da wannan mummunan al’amari, tsaron al’ummar Igbo a Kebbi ya na cikin wani hali. Mun samu bayanai da dama da ke bayani dalla-dalla kan munanan yanayi da ’yan kasuwar kabilar Ibo ke fuskanta, inda aka tauye mu su harkokin kasuwancin su saboda barazanar da Lukurawa ke yi mu su.

Sai dai Ohanaeze, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta fara aiki tare da bayar da goyon baya ga karamin ministan tsaro, Dakta Bello Matawelle, yayin da yake gudanar da aikin maido zaman lafiya a yankin.

Kungiyar ta lura cewa bai kamata ‘yan Najeriya su raina yuwuwar karfin wannan kungiya na fadada cikin sauri ba.

Tarihi ya nuna mana cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, masu tayar da kayar baya za su iya rikidewa da sauri zuwa kungiyoyi masu fafutuka daban-daban da ke cin karensu babu babbaka, suna lalata rayuka da dukiyoyin da ba su ji ba ba su gani ba, da hargitsa dukkanin yankuna.

Don haka muna kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya dauki matakan da suka dace don tattara dukkan muhimman albarkatu tare da hada kai da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, don tabbatar da cewa duk dabarun da soja za su yi, suyi domin kawar da ƙungiyar ta’addanci cikin gaggawa,” in ji Ohaneze Ndigbo.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button