Ƙasashen Musulmi sun fara taro kan yaƙin Gaza da Lebanon a Saudiyya

Spread the love

A yau Litinn ne aka fara taron ƙasashen Musulmi da Larabawa wanda Saudiyya ke karɓar baƙunci, domin tattauna batun yaƙin da Isra’ila ke yi da Hamas a Gaza da hare-haren da take kai wa a Lebanon.

Ministan harkokin waje na Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al-Saud shi ya shugabanci taron share fage na ministoci wanda ya shirya ajandar da za a tattauna, bayan da gwamnatin ƙasarsa ta kira taron ƙolin don bincike kan rikicin Isra’ila da Hamas a Gaza da kuma na Hezbollah a Lebanon, inda yanzu taron ke gudana a Riyadh.

Taron na yanzu a cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar zai ɗora ne a kan abubuwan da aka tattauna a taron da shugabannin ƙasashen Larabawa da Musulmi suka yi a babban birnin na Saudiyya a shekarar da ta wuce.

Haka kuma taron zai mayar da hankali sosai wajen samar da tartibiyar hanya da za a bi domin kawo ƙarshen yaƙin na Gaza da kuma na Lebanon kamar yadda Saudiyyar ta sha alwashin yin duk abin da ya wajaba don cimma wannan buri.

Saudiyya ta shirya wannan taron ne bayan da a baya-bayan nan da karɓi baƙuncin wani taro na farko na haɗakar duniya domin matsa lamba ta ganin an samar da ƙasar Falasdinu.

Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar ta ce ana sa ran shugaban ƙasar Bola Tinubu wanda ke wajen taron zai gabatar da jawabi a kan kawo ƙarshen rikicin na Gaza da Lebanon.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button